Har yanzu dan wasan tsakiya na Ingila, Mason Mount, bai amince da sabon kwantiragi a Chelsea ba, bayan tattaunawa kan zai karasa watanni 18 da suka rage kafin karewar kwantiraginsa.
Paris St-Germain ka iya dauko dan wasan gaba na Tottenham Son Heung-min, sakamakon shakkun da Real Madrid ke yi kan daukar dan wasan mai shekara 30, dan asalin Koriya ta Kudu. (El Nacional)
Manajan Liverpool Jurgen Klopp ya ce suna tattaunawa kan kara tsawon kwantiragin dan wasan gaba Roberto Firmino, mai shekara 31, a yayin da kwantiragin dan wasan dan kasar Brazil ke karewa a bazara. (Liverpool Echo)
Mai tsaron ragar Manchester United David de Gea, dan shekara 32, zai fuskanci rage albashi na akalla fam 100,000 a mako idan har yana son ci gaba da zama a kulob din. (Daily Star on Sunday)