An yi Kira ga matasan kasarnan kan su tashi tsaye suyi amfani da damar su wajen tsayawa da kafafunsu domin dogaro da kansu ta hanyar samun ayyukan yi, don gujewa shiga ayyukan batagari.
Kiran ya fito ne daga bakin Sakataren kungiyar kasuwar abinci ta duniya dake Dawanau a karamar hukumar dawakin tofa, Garkuwar matasan Arewacin kasarnan, Kwamared Rabiu Abubakar tumfafi a bikin nada shi a matsayin Garkuwar matasan Arewacin kasarnan, da kungiyar wayar da kan matasa ta arewa ta yi masa, tare da bashi lambar girmamawa da ya gudana a nan kano.
Tumfafi ya ce, yanzu lokaci ya sauya da yakamata matasa, su zamto masu neman na kansu domin zama jakadu na gari a cikin alumma, ta yadda za,a yi alfahari da su a koina a fadin Duniya.
Kwamared Rabiu Abubakar tumfafi, yace, rashin yin sana,a duk kankantarta yana daga. Cikin abubuwan da suke
Haifar da shiga munanan ayyuka da suka Hadar da sace, sace da kwacen wayoyi Wanda ya kan kai ga har su raunata mutum.
Ya kuma shawarci yankasuwa musamman, Gwamnati da masu ruwa da tsaki da masu hannu da shuni da su tallafawa matasa wajen ganin sun samu sanaoin da Zasu dogara da kansu, domin kaucewa munanan dabiu.
A jawabinsa Shugaban kungiyar wayar da Kan matasan Arewacin kasarnan, sanata Usama Galadima, Wanda kakakin kungiyar, Ambasada Mahmud said, ya wakilta, yace kuginyar ta karrama Abubakar Tumfafi ne, bisa jajircewar da yake da ita da tallafawa matasa da dalibai wajen ganin sun dogara da kawunansu ta fannoni da dama da biya musu kudaden karatu da sauran abubuwa.
Daga nan ya bukacesa daya yi amfani da wannan dama domin ci gaba da wayar da kan matasa da tallafa musu a kodayaushe domin su zamto Manyan jakadu na gari a jihar nan da ma kasa baki daya.
Da yake Karin haske ga matasa da daliban kasar nan, Kwamishinan kimiyya da fasaha na jihar Kano, Alh idris Garba, Ya bukaci kungiyar da ta kara zage damtse wajen ganin ta ci gaba da wayar da kan matasan Arewacin kasarnan, ta yadda zasu yi amfani da wayoyin hannu da naura mai kwakwalwa wajen samarwa kawunansu abubuwan yi da za su dogara da kawunansu, kasancewar ayyukan yi sun yi karanci a kasarnan.
Kwamishinan yace wayoyin hannu, ba Wai kawai za, a yi amfani da su bane wajen Sada zumunci kadai Ba, har ma da Samar da ayyukan yi a zamanance.
Haka zalika, ya kara da cewa, Gwamnatin jihar Kano, ta kafa cibiyar koyan Sana, oin dogaro da Kai a hanyar Zaria ga Daliban da suka kammala karatu basu samu aiki ba, inda yace, wannan cigiya tana koyar da sanaoi daban daban domin rage marasa ayyukan yi.
Ya kuma shawarci, Kwamared Rabiu Abubakar tumfafi, daya kara himma wajen tallafin daya Saba yi, domin irin jajircewar da yake da ita da gudunmawar da yake bayarwa ga matasan kasarnan, ya sanya suka nadashi a wannan matsayi.
Ibrahim Sani Gama pyramid radio.
Garkuwan ya godewa Allah subhanahu wataala bisa wannan nadin nasa, ya kuma bayyana farin cikinsa bisa wannan rana da Allah ya nuna masa.
Tumfafi ya godewa majalisar wayar da kan matasan Arewacin kasarnan bisa wannan karimci da ta yi masa, inda yayi musu fatan alheri tare da adduar samun nasara a dukkannin manufofi da nasarorin data sanya a gaba.