Hukumar kula da ‘Yan gudun hijira ta Majalisar dinkin Duniya tace adadin mutanen da suka gudu daga yankunan da ake fama da tashin hankali da wadanda suka gudu daga inda ake cin zarafin Bil Adama da kuma azabtar da su a karon farko ya zarce miliyan 100 sakamakon karin mutanen da aka samu dake tserewa daga rikicin Ukraine da kuma wasu tashe tashen hankula.
Hukumar tace wannan adadi zai tada hankalin kasashen duniya da kuma kokarin kawo karshen wasu daga cikin wadannan tashe tashen hankulan dake tilastawa mutane tserewa daga gidajen su.
Sanarwar Hukumar yace ya zuwa karshen shekarar 2021 alkaluma sun nuna cewar ana da mutane kusan miliyan 90 da suka gudu daga matsugunan su sakamakon rikice rikicen da ake yi a kasashen Habasha da Burkina Faso da Myanmar da Najeriya da Afghanistan da kuma Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo.
Hukumar tace mamayar da Rasha ta yiwa Ukraine a ranar 24 ga watan Fabarairu ya sanya akalla mutane sama da miliyan 8 barin gidajen su, yayin da sama da miliyan 6 daga cikin su suka gudu suka bar kasar su.
Shugaban Hukumar Fillipo Grandi ya bayyana wannan adadi a matsayin mai tada hankali wanda bai dace ace an samu haka ba, inda ya bukaci daukar matakan gaggawa domin samo hanyoyin kawo karshen wadannan tashe tashen hankulan dake tilastawa mutane barin gidajen su.
Wannan adadi na miliyan 100 ya zarce kashi guda na yawan mutanen dake fadin duniya, kana kuma kasashen duniya 13 ne kacal ke da yawan mutanen da suka zarce wannan adadi