Rashin aiki ya ƙaru ga matasa a kasar China inda ya yi munin da ba a taɓa gani ba tun bayan da ƙasar ta fara farfaɗowa daga koma bayan da cutar korona ta haifar.
Rashin aikin ya fi yawa ne a tsakanin matasa ƴan shekaru 16 zuwa 24 da ke rayuwa a manyan biranen ƙasar inda adadinsu ya kai kashi 21.3 a watan da ya gabata, kamar yadda bayanai a hukumance suka nuna.
Hakan na zuwa ne a yayin da ƙasar da take ta biyu a ƙarfin tattalin arziki a duniya, ƙarfin tattalin arzikinta ya ƙaru da kashi 0.8 a cikin watanni uku zuwa karshen watan Yuni.
Masu sharhi na cewa ana sa ran hukumomin ƙasar su fitar da sababbin matakan haɓɓaka tattalin arzikin ƙasar.