Babbar kotun tarayya dake zamanta a jihar Kano ta umarci gwamnatin jihar da ta biya tarar Naira miliyan biyu ga wasu mutane biyu da tayi yunkurin rusa wa Gidaje a Unguwar Salanta
Kotun da mai sharia, Simon Amobeda ya ke jagoranta a hukuncin da tayi ta ce mutane suna da ikon mallakar gurare ta hanyar da ya dace
Kazalika kotun ta umarci gwamnatin Kano ta gyara katangun da hukumar KNUPDA ta yiwa fenti tare da rubuta alamar a cire ginin.