Wata jaririya ta kubuta bayan da hayaki ya kashe iyaye da ahlin ta

Anambra – Jami’an ‘yan sandan jihar Anambra sun tabbatar da mutuwar ma’aurata, ‘ya’yansu biyu da ƙarin wasu mutanen biyu a yankin Nkwele Ezunaka da ke garin Onitsha.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa ma’auratan, ‘ya’yansu biyu, surukarsu da kuma mai taya su aiki sun rasu ne ranar Laraba, sakamakon shaƙar hayaƙin janareto da suka yi.

Rahoton ya bayyana cewa ma’auratan sun tare ne a sabon gidansu wanda mijin ya yi wa matarsa kyauta ta murnar sabuwar haihuwa da ta yi.

A cewar rahoton lamarin ya faru ne a daren farko da suka shafe a sabon gidan, inda jaririn ne kawai daga cikinsu ya rayu.

An samu cewa wani daga cikin abokan mai gidan ne da bai samu damar zuwa murnar a daren ba ya zo gidan da safe, inda ya tarar da ƙofofin gidan a rufe, a yayin da janareton kuma yake a kunne.

Maƙwabtansu sun kawo ɗauki bayan sanin halin da ake ciki Mutumin ya yi ƙoƙarin sanar da maƙwabtan mamatan, waɗanda da taimakonsu ne aka yi nasarar ɓalle ƙofar, inda aka tarar da su kwance, wasu ba bu rai wasu kuma sun jigata.

Mutumin ya ce an yi ƙoƙarin kai matar da kuma ɗiyarta guda ɗaya asibiti, inda daga bisani aka tabbatar da cewa suma sun rasu kamar yadda jaridar The Guardian ta wallafa

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments