Lamarin ya faru ne a patakwal babban birnin jihar Rivers yayin da wata karamar hatsaniya tayi sanadiyar matar mai suna Abigail ta gaza mallakar zuciyar ta inda ta chaka wa yarinya yar shekara 12 mai suna Oluebube, wuka.
A cewar yaya ga Oluebube, tana wanki ne a rashin sani ta watsa wa Abigail ruwan dauda ita kuma tayi gajab Hakuri inda ta biyeasa son zuciya tayi wa kanwar ta aika-aika ta hanyar chaka mata wuƙa
Rundunar yan sanda ta kasa reshen jihar Rivers ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin mai magana da yawun ta.