Mai girma Abba Kabir Yusuf ya yi magana a game da rushe wasu gine-gine da gwamnatinsa ta ke yi, ya bayyana dalilin da ya sa aka kama wannan layi. Da yake jawabi a garin Kano,
Jaridar Legit.ng Hausa ta ruwaito Gwamna Abba Kabir Yusuf ya na kokawa a kan yadda aka rika cinye filayen makarantu.
Gwamnan ya zargi gwamnatin Abdullahi Ganduje da shiga cikin makarantu, ta saida filaye, ya ce mai dakin tsohon Gwamna ce ta mallaki mafi yawan filayen
Da yake jawabi a Africa House a ranar Lahadi, sabon Gwamnan ya sha alwashin fitar da sunayen mutanen da aka yanki filayen makarantu aka saida masu.
A cewarsa, wasu daga cikin manyan mutanen da su ka amfana da wannan badakala da aka yi ne su ke fitowa su na suratai domin tunzura mutanen Kano.
Abba Yusuf yace maimakon a gina dakunan karatu da wurin kwanan dalibai, sai gwamnatin da ya gada ta rika amfani da filayen domin kashin kan ta.
Gwamnan ya nuna ba zai bari a cigaba da tafiya a haka ba, zai dawo da duk filayen al’umma.
Makeken fili a makarantar Legal har da dakin karatu a wurin, ya je ya kwace, ya yi fulotai na alfarma a ciki, 70% na goggo ne da ‘ya ‘yanta.