Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, ya kai wa shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ziyara a Ofishinsa da ke Villa ranar Jumu’a, 15 ga watan Yuni.
Da yake hira da manema labarai, Matawalle ya kwatanta wannan ziyara da ya kai wa Tinubu da, “Ziyarar ɗa ga mahaifinsa.
” Ya ce shugaba Tinubu ya fara nuna wa duniya cewa yana da duk wata kwarewa da ake buƙata ta jan ragamar Najeriya.
Matawalle ya kara da nuna yaƙinin cewa Tinubu zai kafa tarihin zama shugaban ƙasan da ba’a taɓa kamarsa ba a tarihi.
“Komai na tafiya daidai zuwa yanzu, kunga yadda shugaban kasa ya kinkimo aiki tun farko, to wannan ba sabon abu bane a wurinsa, shugaba ne nagari mai tsaruka masu kyau, zai cika alƙawurran da ya yi a kamfe.”
“Bayan ganin kamun ludayinsa, da yawan mutane sun aminta cewa Najeriya zata zama ƙasar da ba bu kamarta a nahiyar nan. Ina da yaƙinin Asiwaju zai zama shugaban da ba’a taɓa kamarsa ba a kasar nan.”