Yadda sojoji suka kashe wani jagoran masu garkuwa da mutane a Kaduna
Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kashe wani jagoran yan taadda mai suna Isyaku Danwasa.
Rundunar ta bayyana hakan ne a shafin ta na Twitter wanda laftanal kanal Musa Yahya ya wallafa
Sanarwar tace jami’an sojin sun Sami bayanan sirri akan yan ta’addan kafin faruwar lamarin kuma suka rutsa su a gurin da suke sayen alburusai inda suka harbe su a take a gurin.
Rundunar ta ce an Sami Bindugu kirar Ak 47 da alburusai masu yawa da kuma kudi Naira 200,000 sai mashin guda daya da aka kone shi
A nasa bangaren shugaban dake kula da ayyukan rundunar. Manjo Janar Taoreed Lagbaja ya yaba da kokarin jami’an kuma yace ba zasu ragawa duk wani Dan taadda ba