Rundunar yan sanda ta kasa reshen jihar Naija ta nemi shugaban jami’ar IBB, Ibrahim Badamasi Babangida ya sahale mata domin gudanar da bincike a Dakunan kwanan daliban
Rundunar ta nemi hakan ne a wata wasika da ta aika wa IBB mai dauke da sa hanun babban Baturan yan sanda na Lapai, Yusuf Musa,
Musa yace sun ga dacewar hakan ne bayan samun rahoton ayyukan damfarar yanar gizo daga hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC
Kana ya ce rundunar su zata gudanar da bincike ne kadai a Dakunan kwanan daliban da wayoyin hannuwan su ba tare da aiwatar da wani abu na cin zarafi ba