An tsare dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi a birnin Landan, na kasar Birtaniya inda ya je bikin Easter Monday kamar yadda kakakin kungiyar kamfen din Obi-Datti, iran Onifade, ya bayyana.
Sanarwar tace jami’an hukumar kula da shige da fice na Landan sun ci zarafin Obi sannan suka tsare shi,
A cewarsa, Obi ya isa filin jirgin sama na Heathrow da ke Landan daga Najeriya a ranar Juma’a, 7 ga watan Afrilu sannan ya bi layi don cike ka’idojin filin jirgin saman lokacin da jami’an suka kama shi sannan suka nemi ya yi gefe.
“An yi masa tambayoyi na tsawon lokaci ya ce hakan bakon lamari ne ga mutumin da ya shafe fiye da shekaru 10 a wannan kasar.