Rukunin karshe na muhajjatan bana daga jihar Kano a kasa Mai tsarki sun kammala ziyarce-ziyarcen guraran tarihi dake garin madina a kasa Mai tsarki
Bayanin Hakan ya fito ne daga bakin shugaban ayarin ‘yan jaridu Kuma Mai magana da yawun gwamnan jihar Kano malam Sunusi Bature Ahmad Dawakin Tofa a kasa Mai tsarki
Dawakin Tofa ya ce rukunin karshe na maniyata daga jihar kano ya Isa kasa Mai tsarki a ranar Alhamis a jirgin Max Air
Ya Kuma godewa hukumar kula da aikin hajji ta kasa bisa kulawa akan mahajjata kama daga gurin zama,abinci da sauran ababan mure rayuwa akasa Mai tsarki
Ya Kuma Kara da godewa gwamnan jihar Kano Engr.Abba Kabir Yusuf bisa tsayawa tsayin daka da kulawa wajen ganin Jin dadin maniyata daga jihar Kano zuwa kasa Mai tsarki
Daga karshe shugaban ayarin ,’yan jaridun ya ce tun ranar asabar data gabata maniyata suka bar birnin madina zuwa garin Makkah domin gudanar da Hajjin bana