Daga ADAMU DABO
Gwamnatin jihar Kano ta jaddada aniyarta na sake Gina sabon shataletale da ta rushe a hanyar shiga gidan gwamnati, zuwa hanyar kan titin gadar Sama dake Na’ibawa
Bayanin Hakan ya fito ne daga gwamnan jihar Kano Engr.Abba Kabir Yusuf a yayin ganawarsa da Mai zanan taswirar shataletalen Edifice kaltume Hana a Saban gurin da za a gudanar da wannan aiki
A jawabinta Mai zanan taswirar ta ce hakika wajen ginin shataletalen ya dace zai Kuma kawatar da zarar an kammala aikin
Ta Kuma godewa gwamnan jihar Kano bisa wannan dama da aka Bata ta amfani da zanan taswirar da ta Yi da jimawa