Mataimakin shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo ya amince wa ‘yan kasuwa su kafa sababbin jami’o’i 36 a kasar nan.
Farfesa Yemi Osinbajo ya bada damar kafa jami’o’in ne a lokacin da ya jagoranci zaman majalisar FEC kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto.
Majalisar zartarwa ta duba takardu 40 daga ma’aikatu, cibiyoyi da hukumomi dabam-dabam, daga nan aka bada lasisin kawo sababbin jami’o’i.
Ministan ya ce a cikin jami’o’in da aka kafa har da wanda za ta rika aiki ta yanar gizo, a karon farko kenan da aka kafa irinta a fadin kasar nan.
An ruwaito Adamu na cewa jami’ar da za a samar a jihar Bauchi za ta taimaka musamman ga matan Arewa da ke Dari-dari wajan gogayya da maza.
A bayaninsa, Ministan ilmin bai fadi sunan jami’o’in da za a kafa ba, illa iyaka ya nuna akwai bukatar karin jami’o’i saboda masu sha’awar karatu.