Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana hakan ne ta bakin Ministan Kudi da tattalin arzikin kasa, Wale Edun inda yace zasu gudanar da jerin taruka domin tattauna batun a tsanaki
Kazalika yace yayin tattanawar za su fitar da farashin da ya dace matatar Dangote ta biya a farashin Naira sannan gwamnatin tarayya ta duba yiwuwar saka tallafin ta ko kuma ta kyale Yan kasa su Saya a farashin da ya fitar
A nasu bangaren dillalan man fetur sun bayyana fatan su ga man da matatar Dangote zata fitar inda suke sa ran yafi na hukumar NNPC tsada.