‘Da ga marigayi sarkin Gobir wanda ‘yan bindiga su ka yi garkuwa da su tare da mahaifin sa ya koka da abin da ya jikuma ya gani a lokacin da suke hannun Yanbindigar
Bayan kashe mahaifinsa yanbindigar sun sako shi ya bayyana cewa dan majalisar da ke wakiltar karamar hukumarsu ta Sabon Birni Hon. Aminu Boza ne ya baiwa ‘yan bindigar umarni su yi garkuwa da mahaifinsa da shi kansa a zunzurutun Kudi har Naira Miliyan biyar domin a tsare mahaifinsa tare da aza masa kudin da bazai iya biya ba har ta kai ga sun kashe shi.
Yace “Hon. Aminu Boza, dan majalisar da ke wakiltar karamar hukumar mu ta Sabon Birni ne ya bada Miliyan 5 ga ‘yan bindigar da su ka yi garkuwa da mahaifin mu domin su kashe shi” Inji ‘dan marigayi sarkin Gobir