Gwamnatin tarayya ta gindaya sharuda uka kafin ta debo ragowar yan kasar da suka makale a Sudan

Gwamnatin tarayya, a ranar Litinin 15 ga watan Mayu, ta gindaya shaarudɗan da wajibi cikasu gabanin kwaso ragowar mutanen da suka maƙale a kasar Sudan.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa GT ta kafa sharuddan ne kan yan Najeriya da sai yanzu suka kawo kansu suna son dawowa gida domin tserewa yaƙin da ya ɓarke a ƙasar Sudan.

Yayin da ake dab da gama aikin jigila, Gwamnatin tarayya ta gindaya sharudda uku kan duk mai son baro Sudan zuwa Najeriya

Hakan ta faru ne bayan wasu yan Najeriya kusan 200 koma sama da hakan sun fito a baya bayan nan suna son dawowa ƙasarsu ta gado, tun bayan fara aikin jigilar zuwa yanzu dai an dawo da sama da mutane 2000 daga Sudan

Sharudan sun kasance kamar haka

1 Wajibi ka ɗauki nauyin kanka zuwa bakin ruwan Sudan
2. Wajihi ya kasance kana da karin shaidar zaman ɗan ƙasa na Najeriya
3. Dole sai kana da sahihin hanyar tuntuba ko mazauni a Najeriya.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments