Darajar Naira kara fadi kurum ta ke yi a kasuwar canji, inda a yau Alhamis aka ji labari an saida Dalar Amurka a kan N950.
The Cable ta ce N950 da aka saida kudin Amurkan a kasuwar canji ya na nufin Naira ta karye da N53 kusan 5.9% a cikin kwanaki.
A farkon makon nan abin da aka saida $1 bai wuce N897 ba, amma zuwa yanzu labarin ya canza kafin a gama kafa gwamnati.
‘Yan canji da ke Legas sun bayyana cewa mutane su na neman Dalar Amurka ido rufe.
Masu harkar canjin kudin su na sayen Dala ne kan N935, su kuma sai su saida ta a kan N950, hakan ya ba su damar cin ribar N15.