Shugabannin kasashen Africa ta yamma sun fara taron ƙoli na ƙungiyar Ecowas a kan makomar Nijar a fadar shugaba Tinubu dake Abuja,
Ƙungiyar ƙasashen ta kira taron ne bayan wa’adin da ta bai wa shugabannin mulkin sojan Nijar na cewa su mayar da mulki hannun hamɓararren Shugaba Bazoum Mohamed ya cika a ƙarshen makon jiya.
Kawo yanzu Shugabannin Saliyo da Guinea Bissau sun isa Abuja a shirye-shiryen fara taron.