Shugabannin ƙasashen Ecowas sun ba da umarni ga dakarun sojin ƙungiyar, su ɗaura ɗamarar yaƙi da Nijar, bayan juyin mulkin sojoji na ranar 26 ga watan Yuli.
Sanarwar da Omar Aliu Toure, shugaban hukumar Ecowas, ya karanta bayan taron sirri da suka gudanar ranar Alhamis, shugabannin ƙungiyar sun ba da umarnin shirya dakarun ko-ta-kwana na Ecowas da yiwuwar tilasta wa Nijar aiki da ƙudurorin ƙungiyar.
Sun cimma wannan matsaya ce yayin wani taron gaggawa da suka gudanar a Abuja.
Cikin sauƙi, ba za a iya fayyacewa ƙarara ba, ko umarnin yana nufin dakarun sojin Ecowas za su auka wa Nijar ne da yaƙi, ko kuma za su ɗaura ɗamara su zauna cikin shiri ne kawai.
Shugabannin sun ce sun yi nazari kan rahotannin jakadun da suka aika, kuma sun yi muhawara cikin tsanaki a kan shawarwarin da manyan hafsoshin tsaron Ecowas suka bayar, da kuma sauran bayanan da hukumar ƙungiyar ƙasashen ta gabatar.
Sun kuma nanata yin Allah-wadai da juyin mulkin Nijar da kuma ci gaba da tsare Shugaba Bazoum Mohamed.
Ƙungiyar ta ce za ta tabbatar da ganin ana aiki da duk ƙudurorinta kuma har yanzu duk ƙofofi a buɗe suke. Shugabannin sun kuma ɗora wa jagororin Ecowas alhakin ci gaba da bin diddigin takunkuman da aka ƙaƙaba wa shugabannin juyin mulki a Nijar.
Haka zalika, sun gargaɗi waɗanda suka ce suna kawo cikas ga ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya a Nijar, su guji yin haka.