Daga Jamila Sulaiman Aliyu
Bukin saukar alqurani Mai tsarki da saukar dala’ilul khairat da diwanil ishiriniya na dalibai mata su sabanin da makarantar sinhajiyya ta garin danbatta ya gudana cikin nasara.
Maidakin mataimakin gwamnan Kano kuma Dan takarar gwamna Dr Nasiru Yusuf Gawuna Hajiya Hafsat Nasiru Yusuf Gawuna ta bayar da gudimmawar atamfofi saba’in ga matan da suka samu nasarar saukar
Wakiyar Mai dakin mataimakin gwamnan malama Wasila Abdullah itace ta mika kyautar a madadin Hajiya Hafsat Nasiru Yusuf Gawuna tare da mika sakon Kiran da tayi ga makarantar bisa ci gaba da bawa mata ilmi domin suma su koyar da ya’yansu domin ilmin addini riba biyu ce shi wato duniya da lahira
Malama wasila Abdullahi ta bayyana Mai dakin mataimakin gwamnan da cewa ta saba kyauta kamar yadda taga Mai gidanta yanayi don haka zata ci gaba da kyautata wa al’ummar jihar Nan fannin daya shafi ilmantar da mata da yara dake fadin jihar Nan.
Kazalika ta kuma bayyana cewa hajiya Hafsat Nasiru Yusuf Gawuna ta godewa gidan kadiriyya daya samar da wannan makarantar dake garin danbatta.