MDD da sauran hukumomin kasa da kasa, sun bayyana damuwa dangane da ta’azzarar rikici tsakanin matasa masu dauke da makamai daga jihar Jonglei a yankin Greater Pibor na gabashin kasar Sudan ta Kudu.
Shirin wanzar da zaman lafiya na MDD a Sudan ta Kudu (UNMISS), da takwararta ta Tarayyar Afrika a kasar, da Tarayyar Turai da sauran hukumomin yankin, sun bukaci bangarori masu ruwa da tsaki su ajiye makamai nan take, su kuma kai zuciya nesa tare da girmama hakkokin bil adama.
Wata sanarwar hadin gwiwa da hukumomin suka fitar, ta ce yayin da kare fararen hula ya kasance hakkin da ya rataya a wuyan gwamnatin riko na kasar, a shirye UNMISS da sauran hukumomin suke, su bayar da dukkan taimakon da ake bukata na kare fararen hula a yankunan rikicin.
Sun kara da cewa, ta’azzarar lamarin ta haifar da asarar rayuka yayin da aka samu rahoton ana amfani da manyan makamai. Sun kuma yi kira ga shugabannin kasar su gaggauta kawo karshen rikicin domin tabbatar da tsaron fararen hula tare da bayar da damar kai agaji ga mutanen da rikicin ya rutsa da su.