Firaministan kasar Georgia, Irakli Garibashvili ya bayyana cewa albarkacin magungunan da ake karba daga kasar Türkiye, farashin magunguna a kasarsa ya ragu da kashi 60 zuwa 80 cikin 100.
Garibashvili ya kimanta shekarar 2022 a Georgia a cikin jawabin da ya gabatar a Ginin Gwamnati a babban birnin Tbilisi.
Da yake bayyana cewa Georgia na da matsaloli da mutuncin yankinta, Garibashvili ya bayyana cewa mutanen Abkhazia da Ossetia ta Kudu, wadanda suka aiyana ‘yancin kansu daga kasar ba tare da shawarar kowa ba da goyon bayan Rasha, suna rayuwa cikin mawuyacin hali.
Da yake bayyana cewa za su ci gaba da yin amfani da hanyoyin lumana don dawo da martabar yankunan kasar, Garibashvili ya ce, suna shirin zuba babban jarin tattalin arziki a Abkhazia da Ossetia ta Kudu idan har an maido da yankin.
Dangane da sauye-sauyen da suka aiwatar a fannin kiwon lafiya, Garibashvili ya bayyana cewa, sun bude kasuwar sayar da magunguna masu inganci da ake karbowa daga Türkiye domin rage tsadar kayayyaki a fannin harhada magunguna a Georgia.
Garibashvili ya kara da cewa tun farkon wannan shekarar suka fara shigo da magunguna daga kasar Türkiye.
Ya ce, “Bayan bude kasuwar Türkiye (ga Georgia), mun samu damar rage farashin magunguna sosai da kashi 60 zuwa 80.”