Daga khadija Salisu Danmaliki
Jawabin bankwana da shugaban Najeriya mai barin gado, Muhammadu Buhari, ya gabatar a safiyar Lahadi cike yake da alfahari da kuma neman afuwar ‘yan ƙasa game da rayuwar shekara takwas a ƙaragar mulkinsa.
Ɗaya daga cikin ɓangarorin da shugaban ya ce yana alfahari da shi shi ne zaɓukan da ƙasar ta gudanar a ƙarƙashin mulkinsa – na 2019 da kuma na watan Fabarairu.
“A matsayinmu na ƙasa, wajibi ne mu ɗora a kan nasarorin da muka samu a harkokin zaɓe don Najeriya ta samu matsayin da ya dace a tsakanin ƙasashen duniya,” in ji shi.
“Don tabbatar da cewa dimokuraɗiyyarmu ta ci gaba da inganta kuma ‘yan siyasarmu sun zama adalai, na gina tsarin zaɓen da ƙuri’u ke yin tasiri, sakamakonsa ke da inganci, mai cike da adalci wanda kuma ba a fiya amfani da kuɗi ba. Kuma ‘yan Najeriya za su iya zaɓar shugabannin da suke so.”