An tabbatar da nadin limaman juma’ah na Masallacin Hukumar Hisbah ta jihar Kano Wanda ake saran budeshi ranar juma,ah Mai zuwa.
Babban kwamandan hukumar hisbah sheik Haroon muhd sani ibn sina ya godewa mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado bayero bisa amincewar da yayi na daga likafar masallacin daga na salloli biyar zuwa na juma,ah domin saukakawa dakarun hukumar dama Al”umma makusantan hukumar.
Tunda farko mai Martaba Sarkin Kano Alh Aminu Ado Bayero CFR ya nada limaman masallacin hukumar Ayau labara 18/01/2023 bayan tantancewa daga limamin Kano Prof Sani Zaharaddeen,
Kazalika Mai Martaba Sarki ya amince da nadin limaman na Hukumar Hisbah bisa wakilcin Madakin Kano Alh Yusuf Nabahani Cigari, inda aka nada Mal Makinu Abdulkadir l da Mal Habibu Garba Galadanci II sai Mal Haruna Ya’u Rafin kuka III
Dangane da haka Mai girma babban kwamanda Hisbah Dr H.M.H ibn Sina yake sanar da Al’umma tare da gayyatar Al’umma fadin jihar Nan zuwa bikin bude masallacin a ranar juma’ah mai zuwa 20/01/2023 wacce tayi dai dai da 27/06/1444AH da misalin karfe 1:00 na rana a harabar masallacin hisbah dake sharada
wakiyarmu jamila sulaiman aliyu ta labarta mana cewa a yanzu haka ana dab da bayyana ladanan wannan sabon masallacin na hukumar hisbah idan za,a iya tunawa a kasa shekaru biyu ne hukumar hisbah tayi nasarar samun kotu a hukumar duk da ba ta hukumar bace amma tana saukakawa hukumar shigar da kararraki sannan kuma a yanzu tana dab da fara cin gajiyar masallacin mataimakin shugaban sashin yada labara da fasahar sadarwa O/C sani zailani Arzika yace da zarar an bayyana ladanan zasu bayyanawa al’umma.