Duk Wanda yake da kuri”a bai je zabeba to harga Allah yana da laifi kuma Allah bazai kyale Shiba: Babban limamin ma’aikatar Shari,’a

Anyi ittifakin yan’jaridu daga kafafen yada labarai daban daban zasu taimaka wajen samun zabe Mai cike da nasara.

Cibiya Mai fafutuka wajan ganin an zauna lafiya a fadin kasar nan Mai suna CARDINAL ONAIYEKAN FOUNDATION FOR PEACE Wanda shugabar sashen kula da tattara bayanai Mrs Augustine Richard ta wakilci cibiyar tace taron wayar dakan na wuni guda an gayyaci masana a fannonin da abin ya shafa don ganin anyi zabe Mai cike da dimbin nasara

A nasa bangaren daraktan hukumar wayar dakai NOA Alhaji Salisu waziri kutama ya shawarci wadanda basu da kuri”a dasu zauna a gidajensu maimakon fita filin zabe ko haddasa fitintunun daka iya jefa su cikin halin ni “ya su.

Wakiliyar hukumar zabe ta karamar hukumar fagge Hajiya Maryam Adamu ta bayyana cewa dukkan abin da mutane zasuyi ya hsna ruwa gudu shine ke dakile nasarar zabe tare da Kiran iyaye dasu hana ya”yansu yin ayyukan da zasi janyo musu fadawa hannu jami,’an tsaro a yayin. Zabe domin za’a tattare su ne a rufe sai bayan wani tsawon lokaci sannan a tuna dasu.

Shima a nasa bangaren Malam Haruna muhd Bawa babban limamin ma’aikatar Shari,’a ya yi jawabi Mai tsaho akan harkokin da suka shafi tarayya a addinance har yayi bayanin cewa duk Wanda yake da kuri”a bai je zabeba to harga Allah yana da laifi kuma Allah bazai kyale Shiba Daga cikin wadanda sukai jawabi a wurin taron a kwai postor Emanuel da shugabar kungiyar mata musulmi da wakiliyar civil defense,Aisua yakasai da D P O na fagge da dai sauransu

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments