Kungiyar lauyoyi mata ta kasa reshen jihar kano,ta bayyana mutukar farin cikinta bisa nasarorin ta samu tun ga kafata zuwa yanzu.
Shugabar kungiyar mai kula da al,amuran da suka shafi shirya taruka ta kungiyar, Hajiya Salma Ahmed Danbaffa ce,ta bayyana haka a lokacin da kungiyar take gudanar da malima da taron da ta shirya na kwanaki Wanda ya gudana a nan jihar kano.
Salma Danbaffa ta ce,an shirya taron ne domin baiwa wasu mahimman mutane lambar girmamawa da wayar da kan alumma abin da ya shafi alamuran ‘Ya’ya mata da kananan yara domin ganin an kare musu hakkokinsu yadda yakamata.
Tace,ba da lambar girmamawa na daya daga cikin nasarori da kungiyar ta samu Wanda ta karrama jajartattun ‘ya’yanta da mutane da suke baiwa kungiyar gudunmawa ta bangarori da dama.
Salma Danbaffa ta bukaci yankungiyar da su ci gaba da ba da goyan bayansu domin damar kara daga martabar wannan kungiya ta mata Lauyoyi a fadin kasar nan baki daya.
Kungiyar ta kuma yi kira ga Gwamnatin jihar kano akan ta bijirowa da yankungiyar mangartan tsare tsare da su tallafa musu ta fannin ayyukansu, musamman wajen bayar da kulawa ga hakkokin mata da kananan yara duba da halin da suke ci na rayuwar yau da kullum.
Haka zalika,ta bayyana cewa, kofar kungiyar lauyoyi mata a bude take wajen hada kai ga duk Wanda yake bukatar ba da gudunmawa domin kare hakkokin ‘ya’ya mata a duk lokacin da suka samu Kansu a ciki.