Wata jami’a ta bayar da guraben karatu ga jami’an hukumar Hisbah ta jihar Kano

Daga Jamila Sulaiman Aliyu

Hukumar hisbah ta jihar Kano ta nuna gamsuwarta da tayi guraben karatu da akayi mata a jami,’ar Al-Absar da sauran jami’oin da take da alaka dasu.

Mataimakin kwamandan hisbah a bangaren ayyukan yau da kullum Dr mujahid Aminudden Abubakar shine ya bayyana hakan ga manema labarai a Yayin ziyarar da daraktan Jami”ar Alhaji  Mukhtar ya kaiwa hukumar domin kulla alaka tsakaninsu da Kuma horas da dakarun hisbah domin sanin makamar aiki ta yadda zasu Kara amfanar Al”Umma.

Da yake jawabi Daraktan Al-Absar Mukhtar yace zasu wucewa hukumar hisbah gaba domin samarwa dakarunta guraben karatu daga ko wane mataki na karatu domin cigaban hukumar.

A cewar sa idan dakarun hukumar hisbah suka sami horn da ya dace zasu zamo ababan alfahari a fadin nageria bawai iya ka jihar su ta Kano ba,

Ya Kara da cewa Jami”ar musulumci ta Madina na daka cikin Jami,’oin da suke da alaka dasu kuma zasu samarwa dakarun damar ci gaba da karatun su.

Mataimakin kwamandan ya zaga da bakin sassan hukumar domin su gane wa idanun su irin ayyukan hukumar wadanda suka hadar da bangaren killace barasar da aka kama kafin akai ga fasa ta bayan hukuncin kotu.dr mujahid ya kuma zaga da bakin sauran wuraren da suka hadar da wurin tattara bayanai da wurin shigar da korafi da inda ake kauwame masu aifi

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments