Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na gana wa yanzu haka da tsohon shugaban APC ta ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu da Sakatare, Iyiola Omisore a fadarsa Aso Rock.
Jaridar Punch ta rahoto cewa wannan gana wa na zuwa ne mako ɗaya bayan Adamu da Omisore suka yi murabus daga kan muƙamansu.
Abdullahi Adamu da Omisore sun sauka daga kujerun su na jagorantar jam’iyar APC awanni kaɗan gabanin ranar taron shugabanni da taron majalisar zartarwa (NEC).
Murabus din nasu sun yi shi ne a lokacin da shugaba Tinubu ya je kasar Kenya inda ya halarci taron ƙungiyar tarayyar Afirka kuma tunda ya dawo bai zauna da tsoffin shugabannin ba sai yau Talata, 25 ga watan Yuli.
Tun bayan ajiye mukaman nasu Adamu ya ƙi yarda ya ce komai kan abinda ke faruwa a APC, ya ce a jira sai Bola Tinubu ya dawo Najeriya.
Duk da ba bi bayani a hukumance kan abinda zasu tattaun, ana hasashen wanna gana wa zata maida hankali ne kan batutuwan da shuka shafi abinda ke wakana kan shugabancin APC.