Kungiyar dake kula da gidaje da gine ginen kasuwar kantin kwarai,ta gudanar da taron saukar karatun Alkur,ani maigirma domin Neman samun shugabanni nagari da samun saukin alamura bisa halin matsin rayuwa da alummar Najeriya suke ciki a halin yanzu.
Shugaban kungiyar Alh.Balarabe Tatari,yace akwai gidaje sama da 160. da shugabancinsu dake kasuwar suka sauke kur,ani kamar yadda uwar kungiyar ta bukata Wanda ya gudana a fadin kasuwar baki daya a yau.
Tatari ya bayyana cewa, an gudanar da taron saukar karatun alkur,anin ne,domin Neman gafara ga Allah subahanahu wata,ala bisa kurakuran da alumma suka aikata da kuma,Neman taimakon Allah ya ba mu shugabanni nagari da samun bunkasar harkokin kasuwancin jihar kano da ci gaban tattalin arzikin Najeriya.
Shugaban ya kuma ce,kungiyar kula da gidaje da gine ginen ya jaddada cewa, sakamakon mayuwacin halin da alummar Najeriya suke ciki na rashin zagayawar takardun kudade Wanda ya haifar da matsaloli da dama a bangarori da yawa na harkokin kama,ar kasar nan.
Balarabe tatari, yace malamai da dama da yankasuwane suka halarci wannan taron, Wanda an sauke alkur,ani maigirma da ya kai sau Dari biyu,duk domin Nemawa kasa da alummar Najeriya sauki.
Ya kuma, yi kira ga sauran kungiyoyin yankasuwa na koina dake fadin kasar nan, da su koyi da irin wannan tsari da kungiyar kula da gidaje da gine ginen kasuwar kantin kwari ta gudanar,inda yace,rashin aiwatar da irin wannan ba karamar Marsala bace ba,ga alummar Najeriya, shiya ake ta shiga matsaloli da yawa.
Shugaban yace yakamata alummar Najeriya su koma ga Allah ta hanyar kaucewa saba masa da dogaro a garesa ba wai wani shugaba ba ko waninsa,akwai bukatar alumma su yi taka tsantsan bisa kurakuran da aka gudanar a baya na yakinin wani ne zai magance matsalar halin da ake ciki.
Daga karshe shugaban kungiyar ya yabawa alummar da suka halarci taron da wadanda suka ba da gudunmawar aiwatar da taron saukar karatun alkur,anin.