Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron kasar China, Tan Kefei, ya amsa tambayoyin ‘yan jarida game “balan balanced ta leken asiri” ta kasar.
Kefei a wani taron manema labaru da aka shirya a yau Alhamis yace Yana mai adawa da kalaman rashin gaskiya da wasu mutane ke furtawa a Amurka, tare da fatali da gaskiyar lamari.
Ya ce, tarihi ya tabbatar da cewa zai ci gaba da tabbatar da cewa, a ko da yaushe sojojin kasar Sin sun kasance masu tsayin daka wajen aiwatar da ayyukan tabbatar da tsaro a duniya, da yin hidimar gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bli-Adama.
Ya kara da cewa, kasar Sin a ko da yaushe tana tsayawa kan manufar kasancewa wadda ba za ta taba fara amfani da makaman nukiliya a kowane lokaci, a kowane hali, kuma ta yi alkawarin ba za ta yi amfani da makaman nukiliya ba, ko kuma ta yi barazanar yin amfani da makaman nukiliya a kan kasashen da ba su da makamin nukiliya, da kuma yin barazanar yin amfani da makaman nukiliya kan yankunan da ba su da makamin nukiliya