Nan da shekaru 10 mutum-mutumi zai iya yin kashi 39 cikin 100 na aiyukan gida.
Masu bincike daga Jami’ar Oxford ta Ingila da Jami’ar Ochanomizut a Japan sun tambayi masana na’urar kwakwalwa mai kwaikwayon dab’iun mutane (AI) 65 ra’ayoyinsu game da yadda na’urori masu aiki da kansu za su iya yin aiyukan gida nan da shekaru 10.
Masana 29 daga Burtaniya da 36 daga Japan sun shiga cikin binciken.
A sakamakon binciken da aka buga a mujallar PLOS One, masana sun yi hasashen cewa siyayyar kayan abinci shine aikin da AI za ta fi shafa.
Kula da yara da tsofaffi shine aikin da fasahar AI ba za ta shafa sosai ba.
Masu binciken sun bayyana cewa maza a Burtaniya sun fi son mutum-mutumi ya maye gurbin mutum wajen gudanar da aiyukan gida fiye da mata, kuma akasin haka a Japan.
Amma aiyukan da kwararrun ke tunanin AI za su iya yi ya bambanta.
Dakta Lulu Shi, wacce ke aiki a matsayin mai binciken a Jami’ar Oxford ta ce, “Ana tunanin na’urori za su iya kashi 28 cikin 100 na aiyuka kamar koyar da yara da kula da su.”