An bayyana kasar Türkiye a matsayin kasar da ta kasance ta biyu da ‘yan Rasha suka fi so suje yawon bude ido.
A wata kididdigar da Hukumar Tsaron Tarayyar Rasha ta fitar, tace ‘yan kasar Rasha miliyan 9 da 710 ne suka ziyarci kasashe daban-daban tsakanin watannin Yuli, Agusta da Satumba.
Laakari da kididdigar ya nuna kasar Turkiyya ce ta biyu a cikin jerin kasashen da yan Rasha ke zuwa.