Southampton ta kori kociyanta Ralph Hasenhutt bayan da ta sha kashi 4-1 a hannun Newcastle ranar Lahadi abin da ya sa kungiyar ta ci gaba da zama a matakin faduwa daga gasar Premier. (Athletic – subscription required)
Newcastle United da Aston Villa na sha’awar mayar da Eden Hazard, gasar Premier daga Real Madrid. (El Nacional – in Spanish)
Tottenham na duba yuwuwar sayen dan wasan gaba na gefe na Everton Anthony Gordon, dan Ingila a watan Janairu. (Sun)
Har yanzu Arsenal na sha’awar sayen dan wasan gaba na gefe dan Shakhtar Donetsk da Ukraine Mykhaylo Mudryk. (CaughtOffside)
Dan wasan gaba na RB Leipzig Christopher Nkunku, dan Faransa zai saurara ya ji daga Real Madrid kafin ya yanke shawarar ko ya tafi Chelsea. (El Nacional – in Spanish)
Arsenal na duba sabbin kwantiragin da za ta gabatar wa dan bayanta na Faransa William Saliba, da dan gabanta na gefe dan Ingila Bukayo Saka, da kuma dan gaban ta dan Brazil Gabriel Martinelli. (Fabrizio Romano)
Darektan PSV Eindhoven Marcel Brands ya ce Leeds ta gabatar da tayin fan miliyan 30 da karin alawus-alawus na fam miliyan 11 ga dan wasanta na gaba na gefe dan Holland Cody Gakpo, a bazarar da ta wuce. (ESPN – in Dutch)
Kungiyoyin Premier da dama wadanda suka hada da Everton da Tottenham da kuma Arsenal na sanya ido a kan dan wasan gaba na Lille da Kanada Jonathan David. (GiveMeSport)
Dan wasan Brentford Ivan Toney, na da damar samun shiga tawagar Ingila ta gasar Kofin Duniya har yanzu duk da cewa hukumar kwallon kafa ta Ingila FA na bincike a kansa game da caca. (Sun)
Dan wasan gaba na gefe na Crystal Palace da Ivory Coast Wilfried Zaha, ya ki cewa komai game da makomarsa duk da cewa kwantiraginsa da kungiyar zai kare a lokacin bazara. (Sky Sports)
West Ham na shirin sayen dan wasan gaba na Blackburn Rovers dan Chile Ben Brereton Diaz, a watan Janairu. (Football Insider)
Leeds na kan gaba wajen masu fafutukar sayen matashin dan wasan tsakiya Birmingham dan Ingila George Hall mai shekara 18. (Sun)