Kasar China taci ribar youn Tiriliyan daya da digo 55 kasa da shekara daya a fannin yanar gizo

Cibiyar nazarin masana’antar intanet ta kasar Sin, ta fitar da takardar bayani game da ci gaban tattalin arzikin masana’antar intanet ta kasar, inda ta yi hasashen cewa, darajar masana’antar za ta kai yuan triliyan 4.45 a bana, wanda zai kai kaso 3.64 na alkaluman tattalin arziki na GDP na kasar.

A yanzu, masana’antar ta shiga cikin harkokin tattalin arziki da suka shafi hada-hadar kudade kai tsaye, wanda ya shafi rukunoni 45 na tattalin arzikin kasar.

A shekarar 2021, darajar masana’antar a wannan fanni, ta kai yuan triliyan 2.93, inda aka yi hasashen darajarta a bana za ta kai yuan triliyan 3.16. Baya ga haka, masana’antar na daukaka tsarin samar da ayyukan yi a kasar tare da daidaita ci gaban bangaren.

An yi kiyasin za ta samar da sabbin guraben ayyukan yi fiye da miliyan 1 da dubu 50 a bana.

Gu Weixi, mataimakin daraktan cibiyar nazarin masana’antar intanet ta kasar Sin, ya ce masana’antar ta taka muhimmiyar rawa wajen daidaita tsarin samar da kayayyaki, kuma tana bayar da gagarumin taimako ga bangaren tattalin arziki na zamani.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments