Shugaban kamfanin alkorash travel Agency ya koka dangane da yadda masu sana,ar hada hadar fitar da miniyyata aikin hajji da umara suke fuskatar kalubale saboda rashin kudaden takardun naira a hannun alummar Najeriya.
Shugaban kamfanin, Alh.Fasal sani ne yayi wannan kokawar a lokacin da yake ganawa da manema labarai a ofishinsa dangane da halin da alummar Najeriya suka samu Kansu a ciki na matsin rayuwa.
Faisal sani yace yakamata Gwamnatin Najeriya da sauran masu fada a ji da su yi magana domin Neman hanyoyin da za,a Samar da isassun takardun naira, kasacewar har yanzu mutane suna fama da karancin takardun naira a hannunsu.
Yace, duk da kotu ta ba da umarnin cewa,a ci gaba da hada hada da tsaffin kudaden naira, amma,har yanzu bata sauya zani ba,domin kuwa mutane da dama suna kwana da yunwa da rashin kudaden ma da za su sayi ko ruwa da za su,inda yace wannan ba karamin kalubale bane ga Gwamnati da ma alummar Najeriya baki daya.
Shugaban kamfanin yace, yanzu mutane da suke zuwa umarah suna mutukar koka musu saboda matsalolin rashin kudaden takardun naira da suke fama da shi, su Kansu ajojin da suke sana,ar kai mutane suna fama da wannan yanayi da ake ciki a halin yanzu.
Alh.Faisal sani ya shawarci Gwamnatin Najeriya da Babban bankin kasa akan ya yi iya kokarinsa domin buga sabbin takardun kudaden naira isassu domin a samu saukin al,amura yadda suka kamata,musamman duba lokacin hajjin Bana ke karatowa,Wanda yin hakan zai Samar da saukin alamuran yau da kullum.
Yace matasan kasar nan, suna fama da karancin ayyukan yi Wanda hakan na daya daga cikin abubuwan da suke har da matsalolin shaye shayen muggun kwayoyi shiga bangar siyasa ba gaira ba dalili,wannan na gurbata rayuwar matasa.
Shugaban kamfanin ya yi kira ga matasa da su kasance masu Neman na Kansu ta hanyar yin sana,oin dogaro da kai musamman yin kananan sana,oi ba wai sai ayyukan Gwamnati ba,koda ma sun yi karatu,karsu zauna domin jiran sai Gwamnati ta basu aiki.
Daga karshe yace kamfanin Alkuresh Travel And Agency, yace a kodayaushe yana yin abubuwan da za su dadadawa abokanan mu,amullarsa,musammawajen yi musu aiki cikin kwanciyar hankali da lumana,shi yasa mutane da yawa suke son yin Hulda shi,musamman a wannan lokacin ummarah da hajji dake tafe.