Sakataren harkokin waje na kasar Amurka Antony Blinken ya ziyarci Nijar tare da yin alkawarin ba da agaji ga mutanen da suka rasa matsugunansu da kuma tallafawa kokarin kasar na yaki da ta’addanci.
Mazauna babban birnin Yamai da Muryar Amurka ta zanta da su galibi suna da abubuwa masu kyau da suka fada game da ziyarar farko da sakataren harkokin wajen Amurka ya kai a kasar.
“Mun ga yadda a yau sojojin Amurka da ke yankin Nijar ke horar da jami’an tsaro da sojoji,” wata mata a birnin Yamai tana shaida wa Sashen Faransancin Afrika na Muryar Amurka. Sai dai ta ce bai kamata a yi hadin gwiwa a fannin tsaro kawai ba.
“Akwai damammakin hadin gwiwa da dama a cikin shirin sauyin yanayi. Haka kuma akwai batun ruwa mai tsafta, akwai abubuwa da yawa,” inji ta.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken Na Ziyarar Aiki A Nijar
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken Na Ziyarar Aiki A Nijar
Blinken ya yi amfani da wannan tafiya wajen sanar da tallafin dala miliyan 150 a cikin sabon taimakon jin kai don taimakawa wajen biyan bukatu a yammacin Afirka da tsakiyar Afirka da kuma yankin Sahel da rashin zaman lafiya ya haifar.
Bayan taimakon gaggawa ga ‘yan gudun hijira da sauran kungiyoyi masu rauni, Amurka ta kuduri aniyar saka hannun jari kan dorewar zaman lafiyar yankin, in ji Blinken.
Amurka za ta taimaka wajen karfafa guiwar hukumomin binciken manyan laifukan a Nijar domin yakar ta’addanci, da karfafa tsaron iyakoki, da inganta hanyoyin yaki da safarar miyagun kwayoyi, da dakile fataucin mutane, da kuma taimakawa wajen gudanar da bincike, gurfanar da su gaban doka, da kuma rage ta’addanci da tsattsauran ra’ayi,” in ji Blinken yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa tare da takwaransa na Nijar a Yamai.