Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, JP ya bukaci al’uma suyi amfani da damar da suke da ita na zabar shigabanni nagari wadanda zasu jagoranci al’uma.
Sarkin yayi wannan kira ne a lokacin da yake gabatar da wani jawabi na musamman ga manema labarai a fadarsa.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci al’uma dasu zauna lafiya a lokutan babban zabe na kasa da za’a gudanar a ranar asabar mai zuwa.
Sarkin yace sai da Zaman lafiya ne ake iya aiwatar da komi, a don haka ne ya bukaci matasa su kaucewa furta munanan kalamai da amfani muggan makamai tareda shan kayan maye da dukkan wani abu daka iya jirkitar da hankalinsu domin kaucewa abubuwan da basu kamata ba.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya sake jaddada bukatar Hakimai da Dagatai da masu anguwanni su cigaba da wayar dakan al’umarsu muhimmacin Zaman lafiya.
Yayi kira ga jami’an tsaro dasu cigaba dasa ido akan dukkan wanda ya aikata wani lafi tareda hukuntashi
Alhaji Aminu Ado Bayero yayi addu’ar samun zabin shugabanni nagari a dukkan matakan zabubbukan da za’a gudanar a fadin kasar nan.