Yadda Jamian tsaro suka kubutar da mata tara da ake kokarin safarar su

‘Yan-sanda sun ceto mata tara da za a yi safararsu zuwa Libya a Jihar Katsina.
Daga Walid Hari.
Kakakin rundunar ‘yan-sandan JIhar Katsina, SP Gambo Isah, wanda ya bayyana haka, ya ce sakamakon bayanan sirri da suka samu ne jami’ansu suka yi wa wata maboya ta masu safarar dirar-mikiya a yankin karamar hukumar Daura inda suka ceto matan.
kakakin ya yi bayani kan matan inda ya ce, ”wadanda aka ceyo su ne Timilaye Ojo mai shekara 26 daga Jihar Lagos da Blessing Joseph mai shekara 19 daga Jihar Edo da kuma Khadija Abdullahi mai shekara daga Jihar Ondo.
“Haka kuma akwai Safiyyat Ahmed mai shekara 21 daga Jihar Lagos da Precious Nuhu mai shekara 22 daga Jihar Kaduna da kuma Bolanle Adewusi mai shekara 32 daga Jihar Ogun,” in ji shi.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments