Daga Walid Hari.
An yi wa dan wasan Portugal mai shekaru 37 da ke buga tsakiya Cristiano Ronaldo, tayin samun daman raba gari da Manchester United ta hanyar tafiya Inter Miami, kungiyar tsohon abokinsa a harkar tamaula David Beckham. (Star)
Kungiyar Barcelona da ke zawarcin É—an wasan baya na farautar É—an wasan Manchester United Diogo Dalot, mai shekara 23. (Sport)
Southampton na farautar É—an wasan Celtic, Filipe Jota, mai shekara 23. (Football Insider)
Paris St-Germain na duba hanyoyi dawo da É—an wasanta Adrien Rabiot, mai shekara 27, da kwantiraginsa ke kan karewa Juventus. (Fichajes)
Manchester United na Shirin ganawa da wakilan Alejandro Garnacho mai shekara 18 É—an Argentina. (AS via Sport Witness)
Dan wasan Roma Tammy Abraham, ya ki nuna ba lallai ya sake dawowa Chelsea ba a nan gaba.(90 Min)
Arsenal ta fuskanci babban koma baya wajen cefanan É—an wasan Juventus mai shekara 24, Manuel Locatelli, bayan É—an wasan asalin Italiya ya zabi ya zauna a Turin.
Subscribe
Login
0 Comments
Oldest