Rushewar gini tayi sanadiyar rasa rayukan mutane biyu a jihar Kano.
Lamarin ya faru ne a hauren gadagi dake unguwar kofar mata
Jami’in hulda da jama’a na Hukumar kashe gobara ta jihar Kano Alhaji Saminu Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Abdullahi yace tun waje karfe 11:00 suka sami Kiran waya daga wani bawan Allah mai suna Jamilu Salisu Zango in yace wani gini mai girman 50 by 40 ya rushe da mutane uku a take muka tura jami’an mu kuma aka fito dasu aka garzaya Asibitin Murtala daga bisani aka tabbatar mutum biyu sun rasu.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa wadanda suka rasa rayukan su daya Dan shekara 15 dayan kuma Dan shekara 11.