Hukumar NEMA mai bada agajin gaggawa ta tarayyar Najeriya tare da hadin gwiwa da takwararta ta jihar Kano SEMA sun kaddamar da rabon tallafin kayan abinci da na gini ga al`ummomin kananan hukumomin Ajingi da Albasu wadanda suka gamu da ibtilain anbaliyar ruwan sama
Ga dai wasu da ambaliyar ruwan ta yi wa barna kuma suka dace da tallafin gwamnati.
“duk gidana ya zube ba abin da na samu hatta kayan sakawa ta duk sai ba ni aka yi da nawa da na dana, raina ne kawai na yi sa’a na tsira da shi.”
“An ba ni shinkafa da wake da mai da kusa da barko da kuma kwanon rufi.”
Kwamared Sale Aliyu Jili shi ne babban sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano.
“Sako na a nan shi ne su yi amfani da wadannan kayayyakin da aka ba su wajen rage masu radadi duk da dai wanda ya yi hasara irin wannan ba za a iya biyan sa ba. Shi ya sa ya zama wajibi mu kara jan hankalin mutane lallai a gyara magudanan ruwa kuma yanzu za mu shiga yanayin na sanyi a tabbatar dacewa ba a kai wuta daki ba, sannan a rinka kashe wutan lantarki idan za a kwanta barci.”
Su ma a bangaren su shugabannin kananan hukumomin Ajingi da Albasu wuraren da aka kai wannan tallafi, sun yabawa gwamnatin tarayya bisa namijin kokari da ta yi na kawo wannan dauki ga al`umomin yankuna nasu.
“Wannan rana ce mai farin ciki a gare mu saboda tallafin da aka kawo mana wadannan kananan hukumomi ga wadanda Allah ya jarabce su da annobar ambaliyar ruwa.”
Damunar da muka yi ban kwana da ita ta kasance wadda ba za`a iya mantawa da ita ba a kundin tarihi na Najeriya, ganin yadda aka samu ambaliyar ruwan sama a sassa daban daban na fadin duniya wanda kuma hakan ya jefa al`umma da dama cikin rudani.