Tawagar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya dake kasar Mali (MINUSMA) ta bayyana cewa, an kashe sojojinta biyu dake aikin kiyaye zaman lafiya a wani hari da aka kai a arewacin kasar Mali.
A cikin wata sanarwa da MINUSMA ta fitar ta bayyana cewa, a wannan rana a yankin Timbuktu da ke arewacin kasar Mali, wasu da ba a san ko su waye ba, sun kai hari kan tawagar, inda suka kashe dakarun wanzar da zaman lafiya 2 tare da raunata wasu sojojin kiyaye zaman lafiya hudu, daya daga cikinsu ya samu munanan raunuka.
Shugaban MINUSMA, El-Ghassim Wane, ya yi Allah wadai da harin, yana mai jaddada cewa, ya kamata a yi duk mai yiwuwa wajen zakulo maharan tare da gurfanar da su a gaban kuliya.
A watan Yunin bana ne kwamitin sulhu na MDD, ya zartas da kuduri mai lamba 2640, wanda ya kara wa’adin aikin MINUSMA na tsawon shekara guda har zuwa ranar 30 ga watan Yunin shekarar 2023