Tun daga daren ranar Litinin zuwa safiyar Talata, an samu mamakon ruwan sama a birnin Kinshasa, fadar mulkin kasar Congo (Kinshasa), lamarin da ya haifar da ambaliya da zaftarewar kasa a sassan birnin, wanda ya haddasa mutuwar mutane a kalla 141.
A ranar Laraba ne babban sakataren MDD António Guterres, ta bakin kakakinsa, ya mika ta’aziyya ga dangogin mamatan da kuma gwamnatin Congo(Kinshasa) da dukkan al’ummar kasar, inda kuma ya yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki da wuri. A sa’ai daya, kasar Congo (Kinshasa) tana daukar matakai, tare da hada hannu da MDD da abokan hadin gwiwarta da hukumomi masu ruwa da tsaki don shirya ba da tallafin ayyukan ceto.