Hukumar kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta jihar Kano KAROTA tace za ta kama duk Adaidaita Sahun da ke amfani da Gas mai makon fetur
Shugaban Hukumar KAROTA Engr. Faisal Mahmud Kabir ne ya bayyana haka a yau Laraba inda sun yi hakan ne duba da irin haɗarin da gas ɗin ke da shi, zai iya fashewa ta kai ga rasa rayukan al’umma
Yace nau’in gas ɗin da direbobin ke amfani da shi ba shi ne irin wadanda ake amfani da shi a ababen hawa ba
A don haka, ya zama wajibi Hukumar ta kama duk wani matuƙi da aka samu yana amfani da gas ɗin maimakon Fetur
A wani cigaban kuma, shugaban Hukumar KAROTA ya ce an haramtawa jami’an KAROTA yin amfani da Gora a kan titi
Yace daga cikin nau’in horon sanin makamar aiki da ake bawa jami’an za su iya gudanar da aikin su ba tare da amfani da Gora ba
A cewarsa yin amfani da Gora ya saɓa da dokar da ta kafa Hukumar ta shekarar 2012.
Yace babu wani sashin doka da ya bayyana inda jami’an KAROTA za su yi amfani da Gora, “don haka ba za mu sauka daga tsarin doka mu yi abinda ya saɓa da tsarin doka