Kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC, ta bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da labarin yiwuwar dakatar da yajin aikin da ta shirya yi a fadin kasar, wanda aka shirya farawa ranar Laraba.
A daren ranar Talata, kungiyar a cikin wata sanarwa mai cike da rudani dake dauke da sa hannun shugabanta na kasa, Joe Ajaero, ta ce za a gudanar da zanga-zangar kamar yadda aka tsara a manyan biranen Nageriya
Jaridar Kadaura24 ta rawaito tun da fari kungiyar a wata ganawa da tayi da manema labarai a fadar shugaban kasa, babban sakataren kungiyar NLC, Emmanuel Ugboaja, ya bayyana cewa majalisar na iya sake duba matsayar ta a kan shirin yajin aikin, wanda kuma bayanin na Ugboaja ya haifar da cece-kuce a fadin kasar.
Sanarwar wacce aka wallafa a sahihin shafin kungiyar NLC na Twitter, kungiyar ta ce, “Ku yi watsi da jita-jita ta karya, NLC kungiya ce mai haɗin kai kuma mai ƙarfi don haka muna bada tabbacin za a gudanar da zanga-zanga a gobe Laraba a duk fadin Nigeria.”
Hakazalika, mataimakin shugaban kungiyar NLC, Titus Amba, ya bayyana cewa babu wani sabon ci gaba da aka samu biyo bayan jawabin da shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi a yammacin ranar Litinin.
A halin yanzu, NLC na neman a gaggauta sauya duk wasu manufofi da gwamnatin Tinubu ta bullo da su wadanda suka haifar matsin rayuwa ga yan kasa, kamar karin farashin man fetur, karin kudin makarantar gwamnati, sakin albashin malaman jami’o’i da ma’aikata da aka hana na tsawon watanni takwas da dai sauransu.