An yi kira ga Gwamnatin Tarayya kan ta dage yin aikin kidiyar yan kasa da ake shirin yi a watan Mayu, Daily Trust ta rahoto.
Ortom ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya tarbi tawagar kungiyar Middle Belt karkashin jagorancin shugabanta, Dakta Bitrus Pogu, a fadar Gwamnatin jihar dake a Makurdi.
Gwamnan ya ce mutanen jiharsa da dama suna sansanin yan gudun hijira kuma ba za a kirga su ba domin akwai bukatar su koma garuruwansu kafin su samu damar shiga kidiyar.
Ya ce kafin a gudanar da kidaya, dole ne gwamnatin tarayya ta tabbatar da wadataccen tsaro don yan gudun hijira a Benue da sauran wurare a kasar nan su iya komawa gida don a kirga su
“Ina so in ce ya kamata gwamnatin tarayya ta dakatar da maganar kidaya saboda kamar akwai wata manufa. Don haka, sai an samar da tsaro ga duk yan gudun hijira don su koma garuruwansu don bada damar kirga su a mahaifarsu. Saboda abun da na fahimta shi ne hukumar kidaya za ta kirga wanda ke gidajensu,” in ji shi.