Peter Obi, dan takarar jam’iyyar Labour Party a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu ya jaddada cewa babu mai tursasa masa barin kasar
Da yake magana kan kama shi da aka yi a kasar Ingila, tsohon gwamnan na jihar Anambra ya ce jajircewar sa don fitar da Najeriya daga hannun barayi ne ya kawo haka
Ya kuma bayyana cewa ba zai hakura da kudirinsa ba har sai mutanen da ya dauka a matsayin barayi sun bar mukaman shugabanci a Najeriya
Ya kuma sha alwashin cewa jam’iyyar Labour Party ta jajirce don fitar da irin wadannan mutane daga tsarin Najeriya.
Tsohon dan takarar shugaban kasar ya kuma yi alkawarin cewa ba zai yanke kauna da Najeriya ba har sai an fitar da irin wadannan mutane daga mukaman siyasar Najeriya,