A yau Alhamis ne, layin dogo tsakanin kasar China da kasar Laos ya fara zirga-zirgar fasinjoji tsakanin iyakokin kasashen biyu.
China tace tana sa ran lamarin zai bunkasa cudanya da muamala tsakanin kasashe dake yankin.
Da misalin karfe 8 da mituna 8 na safe, agogon Beijing na kasar Sin, jirgin fasinja na farko ya taso daga Kunming, babban birnin lardin Yunnan dake kudu maso yammacin kasar Sin, inda ya nufi Vientiane, babban birnin kasar Laos